Bangaren kasa da kasa, kungiyar kasashen musulmi ta gudanar da wani zama na musamman kan rikicin da yake faruwa akasar Syria, wanda kasashen yammacin turai da kawayensu daga cikin kasashen larabawa suka haddasa kuma suke ci gaba da zuzuta shi.
Kamfanin dilallcin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar yaum sabi cewa, kungiyar kasashen musulmi ta gudanar da wani zama na musamman kan rikicin da yake faruwa akasar Syria, wanda kasashen yammacin turai da kawayensu daga cikin kasashen larabawa suka haddasa kuma suke ci gaba da zuzuta shi tare da bayar da kudade da makamai domin kaddamar da hare-hare-ta yadda za su yi amfani da hakan wajen nuna cewa ana rikici a Syria, kuma su dora alhakin hakan kan gwamnatin kasar.
A bangare guda kuma kungiyar hadin kan kasashen Musulmi OIC wacce ita ce kungiyar kasashen Musulmi mafi girma ta bayyan damuwa kan martanin da kasashen duniya suke bayar wa dangane da rikicin kasar Siriya tana mai cewa ba ta amince da daukar matakan soji kan kasar ba.
Rahotanni daga birnin Jidda na kasar Saudiya wanda kuma can ne hedkwatar kungiyar ta OIC, sun habarta cewa babban sakataren kungiyar Ekmaluddin Ihsanoglu ya fadi a yau cewa kungiyar tana mutunta hurumin kasar da yancinta, ta kuma bukatar dukkan bangarori su taimaka domin warware wannan rikici.
Ihsanoglu ya yi wadannan kalaman ne a zaman taron gaggawa na ministocin kungiyar wanda da ya sami halartar ministan harkokin wajen kasar ta Siriya Walid al-Muallim da takwaran aikinsa na kasar Iran Ali Akbar Salihi.
908478