Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; : jam'iyar Azadi wal adala bangaren siyasa na kungiyar Ikhwanul Muslim a kasar masar bayan bayyana sakamakon zabe a matakin farko sun yi nasara a zaben yan majalisar dokokin kasar Masar kuma a zaben da irinsa na farko tun bayan kifar da gwamnatin Husni Mubarakk.Sakamakon zaben yan majalisa a kasar ta Masar dai ya nuna cewa bangaren siyasa na kungiyar Ikhwanul musulmi ne ya tashi da kashi arba'in cikin dari na kujerun yan majalisar dokokin kasar sai kuma bangaren yan salafiya day a samu kashi ashirin cikin dari na kujerun yayin da sauran jam'iyu day an takara wadanda suka ci nasara a sauran kujerun da aka ware.Tuni masharhanta da al'ummar kasar ta Masar suka fara bayyana ra'ayinsu kan wannan zabe da sakamakonsa.
909662