IQNA

Gabatar Da Taruka Da Jawabai Kan Shahdar Imam Hussain Muhimmi Ne A Wannan Rana

19:10 - December 04, 2011
Lambar Labari: 2234252
Bangaren kasa da kasa, babban malamin addinin muslunci na kasar Bahrain Ayatollah Sheikh Isa Kasim ya bayyana cewa yin jawabai kan shahadar Imam Hussain (AS) da kuma bayyana falsafar da ke tattare da hakan muhimmi ne a cikin lamarin Ashura.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-wifaq cewa, babban malamin addinin muslunci na kasar Bahrain Ayatollah Sheikh Isa Kasim ya bayyana cewa yin jawabai kan shahadar Imam Hussain (AS) da kuma bayyana falsafar da ke tattare da hakan muhimmi ne a cikin lamarin Ashura kuma shi ne hakikanin raya wannan rana.
Shehin malamin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da hudubar Juma’a amsallacin Imam Sadiq (AS) da ke yankin Al-diraz, a gaban dubban masallata, inda ya yi kira da dauki darussan da suke cikin wannan rana, da kuma yin koyi da Imam Hussain (AS) da kuma sauran iyalan gidan manzon Allah a cikin dukkanin koyarwarsu mai tsarki.
Ayatollah Isa Kasim babban malamin addinin muslunci na kasar Bahrain Ayatollah Sheikh Isa Kasim ya bayyana cewa yin jawabai kan shahadar Imam Hussain (AS) da kuma bayyana falsafar da ke tattare da hakan muhimmi ne a cikin lamarin Ashura da kuma raya shi.
909762


captcha