IQNA

Mutane Sattin Ne Suka rasu A Harin Ta'addanci Kan Masu Juyayin Ashura A Afganistan

15:48 - December 08, 2011
Lambar Labari: 2235199
Bangaren kasa da kasa: mutane sama da sattin ne suka yi shahada bayan harin ta'addancin da aka kai masu a ranar ashura a daidai lokacin da suke gudanar da juyayin rashi da zaluntar Imam Huseini (AS) da iyalan gidansa da sahabbansa a yankin Karbala sai gashi wasu yan ta'adda a garin Doshambe na kasar Afganistan sun kai masu hari.




Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: mutane sama da sattin ne suka yi shahada bayan harin ta'addancin da aka kai masu a ranar ashura a daidai lokacin da suke gudanar da juyayin rashi da zaluntar Imam Huseini (AS) da iyalan gidansa da sahabbansa a yankin Karbala sai gashi wasu yan ta'adda a garin Doshambe na kasar Afganistan sun kai masu hari.A wani harin ta'addanci makamancin wannan da aka kai a birnin Kabul wasu fararen hula masu yawan gasket ne suka yi shahada tare da jikkata wasu na daban a daidai lokacin da suke gudanar da juyayin ashura kamar yadda aka kai wani harin ta'addancin a garin Mazarul Sharif inda nan ma wasu suka yi shahada .Wannan dai shi ne karon farko mirinsa tun bayan kifar da gwamnatin Taliban a Afganistan da aka kai way an shi'a a kasar Hari a daidai lokacin da suke gudanar da juyayin ashura kuma tuni yan kungiyar ta Taliban suka ce bas u n eke da alhakin kai wannan hari wani makirci ne na yammaci.

911393

captcha