IQNA

An Yi Allawadai Da Harin Ta’addanci Kan Masu tarukan Ashura A Kasar Afghanistan

16:54 - December 08, 2011
Lambar Labari: 2235215
Bangaren kasa da kasa, ana ci gaba da yin Allawadai da kuma kakkausar suka kan harin ta’addancin da aka kai kan masu gudanar da tarukan Ashura a birnin Kabul na kasar Afghanistan wanda ya yi sanadiyar yin shahadar mutane da dama da kuma jikkatar wasu.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na Afghanpaper cewa, Yanzu haka dai ana ci gaba da yin Allawadai da kuma kakkausar suka kan harin ta’addancin da aka kai kan masu gudanar da tarukan Ashura a birnin Kabul na kasar Afghanistan wanda ya yi sanadiyar yin shahadar mutane da dama da suka hada da mata da kuma kakanan yara.
Wasu rahotanni na daban kuma suna nuni da cewa mutane 28 ne suka yi shahada a yayin da wasu 78 kuma suka ji rauni a wasu jerin hare haren boma bomai a jiya litinin a birnin Bagdaza na kasa Iraqi a tarukan Ashura, majiyar yansanda a birnin ta bayyana cewa hare haren gaba dayansu sun nufi tawaga tawaga na masu juyayin Ashooran Imam husain (a) ne.
Hari na farko ya auku ne a yankin Hilla kilimita 95 kudancin bagadaza inda wata mota ta tashi da boma bomai ta kai mutanen 16 ga shahada a yayinda wasu 45 suka ji rauni, wani likita a asbitin Hilla mai suna Muhammad Ali ya ce sun karbi gawakin mutanen 16 sannan sun bada magani ga mutanen 45, har'ila yau wata majiyar yansanda a birnin ta bayyana cewa wani bom din ya tashi a yankin Aru na arewacin bagdaza ya kai mutanen 8 ga shahada sannan wasu 18 kuma suka ji rauni.
A wani bangare kuma Priministan kasar Iraqi Nuri Almaliki ya bayyana tabbacinsa na samar da zaman lafiya da kuma kawo ci gaba a bangarori daban daban na kasar Iraqi bayan fitar sojojin Amurka daga kasar a karshen wannan watan da muke ciki.
Jaridar washintong Post ta jiya litinin ce ta bayyana wannan labarin kuma ta kara da cewa, Kasar Iraqi zata iya samar da sojoji da jami'an tsaro korarru wadanda zasu ci gaba da tabbatar da zaman lafiya a kasar.
911501

captcha