IQNA

Tsohon Shugaban Lebanon Ya Jinjina wa Sayyid Nasrullah Kan Fitowarsa A Taron Ashura

16:44 - December 11, 2011
Lambar Labari: 2236175
Bangaren kasa da kasa, tsohon shugaban kasar Lebanon Amil Lahud ya jinjinawa Sayyid Hassan Nasrullah babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah kan fitowar da ya yi a tsakiyar masu taron Ashura.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-intikad cewa, tsohon shugaban kasar Lebanon Amil Lahud ya jinjinawa Sayyid Hassan Nasrullah babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah kan fitowar da ya yi a tsakiyar masu taron Ashura a birnin Beirut, duk kuwa da babban hadarin da ke tattare da hakan.
Amil Lahud ya ce fitowar Sayyid Hassan Nasrullah babban kalu bale ne ga makiya wannan al’umma, musamman ma haramtacciyar kasar Isra’ila, wadda take nemansa ruwa ajallo domin kawar da shi saboda kasakancin da ta sha a hannun dakarunsa, kuma ya cancanji jinjinawa kan wannan namijin kwazo da ya nuna.
Tsohon shugaban kasar Lebanon Amil Lahud ya jinjinawa Sayyid Hassan Nasrullah babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah kan fitowar da ya yi a tsakiyar masu taron Ashura da aka gudanar a kasar Lebanon.
Sayyid Han Nasrullah ya gargadi makiya da su kwana da sanin cewa kungiyar hizbullah ta kara karfi da yawa dakaru, haka nan kuma a halin yanzu tana mallakar makamai da za ta iya tunkarar makiya da su.
912268

captcha