IQNA

Kungiyar Hizbullah Ta Mayar Da Martani Kan Zargin Ministan Harkokin Wajen Faransa

14:56 - December 14, 2011
Lambar Labari: 2238825
Bangaren kasa da kasa, kungiyar gwagwarmayar muslunci a kasar Lebanon ta Hizbullah ta mayar da martani kan zargin da ministan harkokin wajen kasar Faransa ya yi da ke cewa kungiyar tana da hannu a harin da aka kai kan dakarun majalisar dinkin duniya da ke kudancin kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin dun Al-manar dake birnin Beirut cewa, Hizbullah ta mayar da martani kan zargin da ministan harkokin wajen kasar Faransa ya yi da ke cewa kungiyar tana da hannu a harin da aka kai kan dakarun majalisar dinkin duniya da ke kudancin kasar a cikin wannan mako.
Bayanin da kungiyar ta fitar kan wannan batu ya ce, bai kamata ji magana ta rashin tunani daga ministan harkokin wajen babbar kasa kamar faransa ba, domin kuwa abin da ya furta dangane da kai harin da aka yi kan dakarun majalisar dinkin duniya akudancin Lebanon ya tabbatar da cewa bai san abin da yake yi ba, kuma ba shi da labarin abin da yake faruwa.
Kungiyar hizbullah ta mayar da martani kan zargin da ministan harkokin wajen kasar Faransa ya yi da ke cewa kungiyar tana da hannu a harin da aka kai kan dakarun majalisar dinkin duniya da ke kudancin kasar a cikin karshen maoon da ya gabata.
914955

captcha