Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani zaman taro na matasa musulmi daga kasashen duniya, da yake da dangantaka da fadakar al’ummar musulmi a wannan zamani wanda cibiyar fadakar musulmi duniya za ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na (islamic – a wakening) cewa ana za a gudanar da wani zaman taro na matasa musulmi daga kasashen duniya, da yake da dangantaka da fadakar al’ummar musulmi a wannan zamani wanda cibiyar fadakar musulmi duniya za ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a cikin wata mai kamawa.
Wannan zaman taro di zai mayar da hankali ne kan muhimman batutuwa da suke da dangantaka da boren da ake fama da shi a cikin kasashen larabawa, wanda sakamakon irin wannan bore ne gwamnatocin kasashen Masar da Tunisia da Libya suka fadi.
Bayanin ya ci gaba da cewa gudanar da zaman taron na matasa musulmi daga kasashen duniya, da yake da dangantaka da fadakar al’ummar musulmi a wannan zamani wanda cibiyar fadakar musulmi duniya za ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa yana da matukar muhimmanci.
915615