Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; an samu wasu takardu kusan na farko farko da aka tarjama kur'ani mai girma a cikin yaren kasar Cana da kuma masu bncike abubuwan al'adu da tarihi na msuulunci suka gano.kamar yadda binciken ya nuna an rubuta wannan tarjama da hannu ta kur'ani mai girma a cikin yaren Cananci na kasar Cana a shekara ta dubu daya da dari tara da goma sha biyu miladiya a garin Lanju da ke lardin Ganshu a arewa masu yammacin kasar Cana.Ding Shiran shugaban mu'assisar kula da al'adu na musulunci da ke karkashin jami'ar Lanju ne ya bayyana cewa: wannan tarjammaman kur'ani da aka samu na nuni da shigar musulunci a aksar da rawar dam asana suka taka a cikin kasar ta Cana.
916797