Bangaren kasa da kasa, limamin juma’a a birnin Beirut na kasar Lebanon ya bayyana cewa, ficewar sojojin mamaya daga kasar Iraki babbar faduwa ce ga manufofin mamaya na kasar Amurka kan wannan kasa ta musulmi da ke da dimbin albartu da arziki da kuma muhimmanci ta fuskoki da dama.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa limamin juma’a a birnin Beirut na kasar Lebanon ya bayyana cewa, ficewar sojojin mamaya daga kasar Iraki babbar faduwa ce ga manufofin mamaya na kasar Amurka kan wannan kasa ta musulmi da ke da dimbin albartu da arziki da kuma muhimmanci ta fuskoki da dama musamman a cikin wannan yanki.
A yau ne sojojin Amurka da ke mamaye da kasar Iraki sun gudanar da biki na musamman wanda ke nuni da kawo karshen mamayar ta tsawon shekaru tara da suka yi wa kasar ta Iraki. A lokacin wannan biki wanda ya gudana a gaban manyan jami'an ma'aikatar tsaron Amurka, sojojin mamayar sun sauke tutatar kasarsu tare kuma da sanya ta a cikin wani dan karamin akwati.
Kamar dai yadda yarjejeniyar da aka sanya wa hannu tsakanin zababbiyar gwamnatin Iraki da kuma kasar ta Amurka, dole ne sojojin na mamaya su fice daga kasar kafin karshen wannan wata na disamba. To sai dai yarjejeniyar ta amince da barin wani adadi na sojojin a matsayin masu bayar da shawara da kuma horo ga dakarun na Iraki.
A tsawon wadannan shekaru 9 na mamaya dai, kasar Amurka kawai ta yi asarar sojojinta akalla dubu hudu da 500 da raunata wasu dubban na daban. To sai dai yanzu haka kungiyoyi na ci gaba da yin kira da a hukuntar tsohon shugaban Amurka Geroge W Bush da mukurrabansa wadanda suka kaddamar da wannan yaki da ya yi sanadiyyar mutuwar Irakawa akalla milyan daya a cikin shekaru tara.
917020