IQNA

Malam Jami’ar Azhar Sun Kira Da A Yi Kisasi Kan Makasan Sakataren Darul Ifta

18:30 - December 19, 2011
Lambar Labari: 2241660
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin fitattun malaman jami’ar Azhar sun fito karara sun kira da a gudanar da kisasi kan wadanda suke da hannu wajen yin kisan gilla a kan babban sakataren ofishin fatawa na jami’ar a dandalin Tahrir.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Yaum Sabi cewa, adadi da dama daga cikin fitattun malaman jami’ar Azhar sun fito karara sun kira da a gudanar da kisasi kan wadanda suke da hannu wajen yin kisan gilla a kan babban sakataren ofishin fatawa na jami’ar a dandalin Tahrir a cikin wannan mako.
Bayanin ya ci gaba da cewa an gudanar da jazanar shaihin malamin wato sheikh Imam Iffat wanda ya rasa ransa a dandalin Tahrir a lokacin da yake halartar gangami na mutanen da suke neman mahukuntan sojin kasar da su gaggauta mika mulki ga hannun farar hula, maimakon ci gaba da yin mulki na angulu da kan zabo.
Dubban mutanen da suka halarci wannan janaza sun yi ta rera taken da cewa sabbin mahukuntan kasar Masar din ne suke da alhakin mutuwarsa, kuma dole a yi adalci wajen gano masu hannu awannan mumman aiki.
Fitattun malaman jami’ar Azhar sun fito karara sun kira da a gudanar da kisasi kan wadanda suke da hannu wajen yin kisan gilla a kan babban sakataren ofishin fatawa na jami’ar a lokacin da yake tare da dubban mutanen da suke nuna rashin gamsuwa da mulkin soji a Masar.
917857
captcha