Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na jaridar Yaum Sabi cewa, palastinawa sun gudanar da zanga-zangar nuna rshin amincewa da matakin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta dauna na hana su yin kiran salla masallatai da nufin takura musu da ma sauran musulmi baki daya da suke zaune a wannan yanki.
A wani labarin kuma ma'aikatar harkokini wajen kasar Labanon ta shigar da kara a hukumance ga UN dangane da irin ayyukan leken asirin da haramtacciyar kasar Isra’ila take ci gaba da yi a kasar wanda ta bayyana shi a matsayin lamarin da ya saba wa kudurin kwamitin tsaro mai lamba 1701 kana kuma barazana ga zaman lafiyar duniya.
Kasar Labanon ta shigar da wannan karar ne bayan da jami'an sojin kasar bisa taimakon dakarun kungiyar Hizbullah suka gano wata na'urar leken asiri da haramtacciyar kasar Isra’ila ta bisne a garin Deir Kifa da ke kusancin kasar a farko-farkon wannan watan.
Gwamnatin kasar Labanon din cikin wannan karar da ta kai haramtacciyar kasar Isra’ila ta kirayi Majalisar dinkin duniya da ta dau matakan da suka dace wajen hana ci gaba da faruwar wannan danyen aiki da yahudawan sahyoniyan suke yi.
Wannan dai ba shi ne karon farko da jami'an tsaron kasar Labanon da kuma 'yan kungiyar Hizbullah din suke kama irin wadannan na'urori da kuma 'yan leken asirin haramtacciyar kasar Isra’ila a kasar ba wadanda suke ta kokari wajen tattaro bayanan sirri dangane da kungiyar gwagwarmaya.
917825