IQNA

Hana Kiran Salla A Masallatan Palastinu Nau’i Ne Na Nuna Wariya

18:58 - December 20, 2011
Lambar Labari: 2242351
Bangaren kasa da kasa, wani marubuci daga cikin haramtacciyar kasar Isra’ila mai suna Yusuf Shaddad ya bayyana cewa irin matakan da haramtacciyar kasar yahudawan take dauka na hana kiran salla a cikin yankunan palastinawa nau’i ne na wariya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alwafd an bayyana cewa fitaccen marubuci daga cikin haramtacciyar kasar Isra’ila mai suna Yusuf Shaddad ya bayyana cewa irin matakan da haramtacciyar kasar yahudawan take dauka na hana kiran salla a cikin yankunan palastinawa nau’i ne na wariya da ake nuna ma al’ummar palastinu a cikin yankunansu da aka mamaye.
Wannan marubuci daga cikin haramtacciyar kasar Isra’ila ya bayyana cewa irin matakan da haramtacciyar kasar yahudawan take dauka da suka hada fada matsugunnan yahudawa, da ma wannan na baya-baya na hana kiran salla a cikin yankunan palastinawa babban zalunci ne a kan hakkoninsu.
Ya kara da cewa babban abin kunya ne yadda kasashen duniya suka shiru da bakunansu kan wannan batu, musamman kjasashen larabawa daga cikinsu, wadanda suke cikin aljihun yahudawa da Amurka.
918648
captcha