IQNA

Gidan Sarautar Saudiyya Na Cikin Rudu Sakamakkon Boren Al’ummomin Larabawa

18:56 - December 20, 2011
Lambar Labari: 2242355
Bangaren kasa da kasa, gidan sarautar Ali-saud da ke mulkin mulukiya akasar Saudiyya na cikin rikici da rudu sakamakon abubuwan da suke faruwa yanzu haka acikin kasashen larabawa da nuna rashin amincewa da mulkin zalunci da danniya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na matasan larabawa masu juyin hali cewa, masarautar Ali-saud da ke mulkin mulukiya akasar Saudiyya na cikin rikici da rudu sakamakon abubuwan da suke faruwa yanzu haka acikin kasashen larabawa da nuna rashin amincewa da mulkin zalunci da danniya irin na shugabannin da sarakuna.
Wani da ya baiwa shugabannin larabawan mamaki shi ne yadda aka kawar da abokan Amurka na kud da kud kamar su Husni Mubarak da kuma zainul abidin na kasar Tunisia, wadanda dukakninsu manyan aminan Amurka da haramtacciyar kasar Istra’ila ne, kuma an kawar ad su ne ta hanyar boren al’ummominsu duk kuwa da kudaden da kasashen larabawan tekun fasha suka fitar domin kare su.
Wani abu da yake daukar hankali yanzu shi ne, yadda irin wadannan kasashen suke gin amfani da wannan damar domin kalubalantar wasu daga cikin gwamnatocin da suke kin mika wuya ga siyatsar Amurka kamar Syria domin ganin bayansu, kuma suke kare wasu da suke dasawa da su duk kuwa da boren da ake yi a kasarsu kamar Bahrain.
918032
captcha