IQNA

An Cimma wata Yarjejiya Tsakanin Kungiyoyi Biyu Na Musulmi A Rasha

13:43 - December 22, 2011
Lambar Labari: 2243239
Bangaren al'adu da fasaha; cibiyar hadin kan musulmi da hadin kan hukumomin musulmi a kasar Rasha da kuma hadin kungiyoyin musulmi a Rasha a matsayinsu na kungiyoyin musulmi mafi girma a wannan kasar sun cimma yarjeniyar aiki tare ta hadin kai tare da sanya mata hannu.



Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: cibiyar hadin kan musulmi da hadin kan hukumomin musulmi a kasar Rasha da kuma hadin kungiyoyin musulmi a Rasha a matsayinsu na kungiyoyin musulmi mafi girma a wannan kasar sun cimma yarjeniyar aiki tare ta hadin kai tare da sanya mata hannu.A ranar ashirin da takwas ga watan azar na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a birnin Masku fadar mulkin kasar Rasha an sa hannu a tsakanin kungiyoyin biyu inda Shaukat Haji Aviyaz uf shugaban cibiyar hadin kungiyoyin musulmi da hukumomin musulmi na rasha ya sa hannu a madadin kungiyar sai kuma Muhammad Haji Rajim Uf shugaban hadin guiwar kungiyar Rasha day a hada da ofishin masu fitar da fatawa a rasha ya sa hannu a madadinsu. Kuma wannan jarjeniyar za ta taimaka a tafiya da ci gaban kungiyoyin musulmi da musulmi a kasar ta rasha da tafiyar da ayyukansu karkashin dokoki da hukumce da karfafa matsayinsu a kasar ta Rasha.


920042

captcha