Bangaren siyasa, diplomasiyar jamhuriyar musulunci ta Iran ta ginu kan bayyana tasirin addinin musulunci a cikin dukkanin sassa na rayuwar zamantakewar mutum saboda haka wajibi ga bangaren diplomasiyya ya zage dantse domin bayyana wannan manufa mai tsarki ga sauran al’ummomi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ofishin jagora cewa, jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Iran Ayatollah Sayyid Khamenei a lokacin da yake zantawa da jami’an diplomasiyyar Iran ya sheda cewa, diplomasiyar jamhuriyar musulunci ta Iran ta ginu kan bayyana tasirin addinin musulunci a cikin dukkanin sassa na rayuwar zamantakewar mutum saboda haka wajibi ga bangaren diplomasiyya ya zage dantse domin bayyana wannan manufa mai tsarki ga sauran al’ummomi na duniya baki daya.
Jagoran ya ci gaba da cewa da dama daga cikin kasashen da suka shedi mikewar al’ummominsu babban abin da ya zaburar da mutanen shi ne addinin muslunci da kuma kishinsa, wanda hakan ke nuni da cewa ko da jagororin kasashen muulmi sun zama ‘yan koren Amurka da yahudawa da sauran makiya muslunci al’ummominsu suna nan da kishi a kan wannan addini mai alfarma.
Daga karshe ya kirayi shugabannin kasashen larabawa da na yankin da su kwana da sanin cewa yin biyya ido rufe ga makiya muslunci ba zai taba kai su ga abin da suke nema ba, domin kuwa makiya muslunci suna kokarin ganin usn gama da su kansu da kuma al’ummominsu. 924748