Bangaren kasa d akasa, haramtacciyar kasar Isra’ila ta mayar da wani masallaci wajen ajiye kayan tarihi a yankin Biri subu da ke gabar yamma da kogin Jordan wanda ke cikin yankunan palastinawa da ta mamaye a cikin shekara ta 1948.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-manar da ke watsa shirinta kan tauraron dan Adam daga birnin Beirut na kasar Lebanon cewa, haramtacciyar kasar Isra’ila ta mayar da wani masallaci wajen ajiye kayan tarihi a yankin Biri subu da ke gabar yamma da kogin Jordan wanda ke cikin yankunan palastinawa da ta mamaye a cikin shekarun da suka gabata.
Bayanin ya ci gaba da cewa an gina wannan masallaci ne a cikin shekara ta 1908, kuma mahukuntan daular Usmaniyya ne suka gina shi, kuma babu wani wanda yake da hakkin ya yi amfani da wannan masallaci baya ga musulmi, domin kuwa mallakinsu ne kuma wurin ibadarsu ne.
Haramtacciyar kasar Isra’ila ta mayar da wannani masallaci ne wajen ajiye kayan tarihi a yankin Biri subu da ke gabar yamma da kogin Jordan wanda ke cikin yankunan palastinawa da nufin tsokanarsu, ta yadda idan suka mayar da martani sai hakan ya zama abin magana daga kashen yammaci.
924758