Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na smc.sd cew, a yau an fara gudanar da wani zaman taro a matsayi na kasa da kasa a birnin Khartum fadar mulkin kasar Sudan da nufin tattauna muhimmancin birnin Qods da matsayinsa ga al’ummar muuslmi na duniya baki daya.
Pira ministan palastinu a yankin Gaza Isma’il Haniyya yana daga cikin wadanda suke halartar wannan taro, bayan ya kammala wata ziyara da ya kai a kasar Masar, inda ya gana da jagororin kasar, da suka hada da mambobin majalisar mulkin soji ta kasar, wadanda suka maye gurbin gwamnatin kama karya ta Husni Mubarak.
A wani labarin kuma haramtacciyar kasar Isra’ila ta mayar da wani masallaci wajen ajiye kayan tarihi a yankin Biri subu da ke gabar yamma da kogin Jordan wanda ke cikin yankunan palastinawa da ta mamaye a cikin shekarun da suka gabata, tun daga shekara ta 1948 miladiyya.
Dangantaka tsakanin palastinawa da yahudawan sahyuniya ne tana kara yin kamari, sakamakon matakan zalunci da gwamnatin yahudawan take dauka kan palastiwa tare da cikakken goyon baya daga kasashen turai.
924787