Bangaren kasa da kasa, jami’ar Azhar da ke birnin ALKAHIRA NA KASAR Masar ta bukaci da a dakatar da watsa shirye-shirye a talabijin din nan na Alkamara na mabiya addinin kirista saboda abin da yake na suka addinin muslunci da neman haddasa fitina a tsakanin mabiyan addinan kirista da musulunci.
Kamfanin diallncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar yau sabi ta kasar Masar cewa, bangaren bincike na jami’ar Azhar da ke birnin Alkahira na Masar ya bukaci da a dakatar da watsa shirye-shirye a talabijin din nan na Alkamara na mabiya addinin kirista saboda abin da yake na suka addinin muslunci da neman haddasa fitina a tsakanin mabiyan addinan kirista da musulunci na duniya, domin kuwa abubuwan da gidan talabijin din yake watsawa sun hannun riga da koyarwar addinin kirista.
Bayanin jami’ar ya ce babban abin da ake bukata a halin yanzu shi ne kara karfafa hadin kai da fahimtar juna tsakanin mabiya addinin duniya baki daya, balantana addininan kiristanci da muslunci wadanda su ne suka fi kusa da juna, saboda haka wajibi dukaknin bangarorin su dakatar da duk mai son tayar da rikici a cikinsu tsakaninsu da wasu addinai.
Jami’ar Azhar ta bukaci da a dakatar da watsa shirye-shirye a talabijin din ta Alkamara ta mabiya addinin kirista saboda a samu zaman lafiya mai dorewa tsakanin bangarorin muslunci da kiristanci, kuma ci gaba da watsa irin wadannan shirye-shirye da tashar ke yi ba zai zama alkhairi ga mabiya addinin kirista ba.
925566