Bangaren al'adu da fasaha:ministan harkokin al'adu na kasar Sudan ya yi nuni da kwarewa da girman da Jamhuriyar musulunci ta Iran take da shi ta fuskar al'adu musamman a bangaren fasaha da kwarewa a harkokin Sinema wakokin yabo don haka kasar Sudan a shirye take ta hada karfi da karfe da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: ministan harkokin al'adu na kasar Sudan ya yi nuni da kwarewa da girman da Jamhuriyar musulunci ta Iran take da shi ta fuskar al'adu musamman a bangaren fasaha da kwarewa a harkokin Sinema wakokin yabo don haka kasar Sudan a shirye take ta hada karfi da karfe da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.Hujjatul Islam da musulmi Said Hamid Malakuti mai kula da ofishin yada al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran a kasar Sudan tare da tawagar da ke mara masa baya a wata ganawa da ya yi da SamuAl Khalfulla Alkarush ministan al'adu na kasar Sudan da kuma tattaunawar da suka yi ne suka dauki matakin fadada dangantakar kasashen biyu na Sudan da na jamhuriyar musulunci ta Iran a harkokin da suka shafi al'adu da zamantakewar al'ummomin kasashen biyu. Da kuma yi wa ministan na Sudan murna da zagayowar irin wannan rana da kasar ta Sudan ta samu yancin kansa.
926152