IQNA

Wata Tawagar Kasar Lebanon Za Ta Nufi Libya Kan Batun Imam Musa Sadr

18:24 - January 08, 2012
Lambar Labari: 2253430
Bangaren kasa da kasa, wata tawagar kasar Lebanon na shirin kama hanya zuwa kasar Libya domin sanin makomar Imam Musa Sadr tare da abokan tafiyarsa da suka ba ta bayan gayyatar da tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar ya yi musu.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadrawa na yanar gizo na jaridar Al-intiqad cewa, ministan harkokin wajen kasar Lenaon ya bayyana cewa wata tawagar kasar na shirin kama hanya zuwa kasar Libya domin sanin makomar Imam Musa Sadr tare da abokan tafiyarsa da suka ba ta bayan gayyatar da tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar ya yi musu shekaru talatin da hudu da suka gabata, kuma tawagar za ta kasance karkashin jagorancin Adnan Mansur.
Wani rahotin kuma yana cewa sojojin gwamnatin kasar Libya sun gudanar da wata zanga zanga a gaban wani reshe na babban bankin kasar da ke birnin Bengaza a jiya Alhamis.
Sojojin suna bukatar sabuwar gwamnatin kasar ta biyasu albashinsu na watannin baya, sannan sun gabatar da kukan cewa mayakan yan tawayen kasar sun mamaye barikokinsu, wanda hakan ya maidasu saniyaea ware a cikin jami'an tsaron kasar.
Sojojin wadanda suka fio cikin kayakinsu na soja kuma rike da bindigoginsu sun yi kira ga sabuwar gwamnatin kasar ta Libya da ta bada karfi kan gina sabowan rundunar sojojin kasar, kan bawa yantawayen kasar wadanda suka kifar da gwamnatin kazzafi kyautan kudade.
Wani daga cikin sojojin mai suna Al-Mubarak Abdullah Al-Oraibi ya fadawa Reuters cewa Mu'ammar Kazzafi tsohon shugaban kasar ya tarwatsa rundunar sojojin kasar a shekarun 1990, kuma ya bawa dakaru na musamman wadanda ya kirkiro don kare mulkinsa karfi mai yawa.
930292

captcha