IQNA

Mai Kula Da Larabawa Da Afrika A ma'aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Yi Allah Wadai da Gina Matsugunan Yahudawa

13:45 - January 10, 2012
Lambar Labari: 2254772
Bangaren siyasa : Amir Abdullahiyan a wata ganawa da yayi da wakilin kungiyar Hamas ya yi Allah wadai da sanarwar da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila na bayyana Kudus a matsayin fadar yahudawa da kuma ci gaba da gina matsugunnan yahudawa.

Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ta watsa rahoton cewa: Amir Abdullahiyan a wata ganawa da yayi da wakilin kungiyar Hamas ya yi Allah wadai da sanarwar da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila na bayyana Kudus a matsayin fadar yahudawa da kuma ci gaba da gina matsugunnan yahudawa.A lokacin wannan ganawar da Huseini Amir Abdallahiyan mai kula da kasashen larabawa da na Afrika a ma'aikatar harkokin wajan kasar Iran a lokacin wannan ganawa day a yi da wakilin kungiyar gwagwarmaya ta Hamas a nan Tehran sun yi bincike da nazarin sauye sauye a Palasdinu da kuma yankin da yadda musulmin yankin suka fara falkawa daga barci a fadin yankin gabas ta tsakiya .Kuma dukansu biyu ne sun ka yi Allah wadai da tofin Allah tsine da wannan matakin takalar fada da gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila ta dauka kuma suka bukaci a taimakawa al'ummar Palasdinu da zabebbiyar gwamnatinsu kai wag a kafa kasarsu mai yancin kai da kwato masu hakkokinsu da doka da dokin kasa da kasa suka amince das u.
931655

captcha