IQNA

Musulmin Amerika Sun Yi Jerin Gwano Nuna Adawa Da Karuwar masu Tsananin Adawa Da Musulunci

15:59 - January 11, 2012
Lambar Labari: 2255668
Bangaren kasa da kasa; musulmi a kasar Amerika musamman da ke birnin Washigton na kasar ta Amerika sun gudanar da gagaramin jerin gwano zuwa majalisar dokokin kasar ta Amerika domin nuna adawarsu da ywaita da karuwar masu tsananin nuna adawa kan addinin musulunci da musulmi kuma sun bukaci ganawa day an majalisar dokokin tare da bukatar kawo karshen wannan matsala da fito na fito da ita.


Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; musulmi a kasar Amerika musamman da ke birnin Washigton na kasar ta Amerika sun gudanar da gagaramin jerin gwano zuwa majalisar dokokin kasar ta Amerika domin nuna adawarsu da ywaita da karuwar masu tsananin nuna adawa kan addinin musulunci da musulmi kuma sun bukaci ganawa day an majalisar dokokin tare da bukatar kawo karshen wannan matsala da fito na fito da ita.Arsalan Bukhari shugaban zartarwa da komitin dangantaka da musulmi a a birnin Washington dangane da wannan lamari ya bayyana cewa; a ranar ashirin da shidda ga watan Dai sun gudanar da wanann jerin gwano a wani mataki na nuna adawa dab akin cikinsu kan karuwar masu bakar adawa da addinin musulunci da kuma musulmi a kasar Amerika kuma a wannan rana ta ashirin da shida ga watan dai na wannan shekara ta dubu daya da darin uku da tis'in za ta zama ranar musulmin jahar Washigton a majalisar dokokin kasar . Kuma kimanin muslmin kasar dari hudu ne za su halarci jerin gwano a wannan rana da ganawa da wakilan majalisar dokokin ta Amerika da bayyana masu koke kokensu da abubuwan da ke ci masu tuwo a kasko.
932197
captcha