IQNA

Kungiyar Musulmi A Nigeria Ta Yi Allah wadai da abin Da Wani malamin Kirista Ya Furta

15:59 - January 11, 2012
Lambar Labari: 2255669
Bangaren kasa da kasa: jama'atun Nasrul Islami a kasar Nigeria ta yi Allah wadai da tofin Allah tsine da abubuwan da malamin kirista ya furta na kokarin da musulmi ke yin a shafe wasu kabilun kasar.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; jama'atun Nasrul Islami a kasar Nigeria ta yi Allah wadai da tofin Allah tsine da abubuwan da malamin kirista ya furta na kokarin da musulmi ke yin a shafe wasu kabilun kasar.Khalid Ali babban sakataren kungiyar ta nasarul Islam a tarayyar Nigeria bayan ya yi nuni da bacin raid a adawar da musulmin kasar ke yi da harin da wasu tsuraru ke kai wa coci coci a kasar da hadarin da ke tattare da hakan ya bayyana cewa; a daidai lokacin da shugabanni da jagororin musulmi a tarayyar Nigeria ke adawa da Allah wadai da kai wa guraren ibada nay an uwansu kiristoci abubuwan da Ayu Uritsujafar shugaban kungiyar kirsitocin Nigeria ya furta na kokarin wasu musulmi na shafe wasu kabilu da mabiya wasu addinai cin fuska da mutunci ne kan musulmin kasar kuma futa irin wadannan maganganu ko kusa ba za su taimaka ba sai kara wa wutar rikici da halin dardar da ake ciki a kasar kawai . Kuma maganganu ne na rashin tunani da tsinkayen nesa.
932383

captcha