Bangaren kasa da kasa, cibiyoyin addinin Musulunci a kasar Iraki sun yi kira da a dauki kwararan matakai domin kaucewa yaduwar tunanin wahabiyanci a tsakanin masu ziyarar a kasar bayan da wasu daga cikin wahabiyawa da Saudiyya ta dauki nauyinsu suke watsa wannan tunani.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na nun cewa, cibiyoyin addinin Musulunci a kasar Iraki sun yi kira da a dauki kwararan matakai domin kaucewa yaduwar tunanin wahabiyanci a tsakanin masu ziyarar a kasar bayan da wasu daga cikin wahabiyawa da Saudiyya ta dauki nauyinsu suke watsa wannan tunani tsakanin mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah.
Bayanin ya ci gaba da cewa da dama daga cikin mutanen da suke yin hakan an dauki hayarsu ne daga gwamnatin wahabiyawan Saudiyya, kuma bay a yada tunanin kiyayya ga iyalan gidan manzon Allah, sun e suke da hannu a dukkanin ayyukan ta'addancin da ke nufar masu ziyara wurare masu tsarki.
Yanzu haka dai cibiyoyin addinin Musulunci a kasar Iraki sun yi kira da a dauki kwararan matakai domin kaucewa yaduwar tunanin wahabiyanci a tsakanin masu ziyarar a kasar bayan da wasu daga cikin wahabiyawa da Saudiyya ta dauki nauyinsu suke watsa wannan tunani na wahabiyanci tsakanin jama.
932580