IQNA

Mai Bayar Da Fatawa A Syria Ya Soki Larabawa Kan Rashin Damuwa Da Yahudantar Da Qods

19:02 - January 11, 2012
Lambar Labari: 2255735
Bangaren kasa da kasa, babban malami mai bayar da fatawar addinin muslunci a kasar Syria ya soki kasashen larabawa kan yadda suka nuna halin ko in kula kan dangane da yadda yahudawan sahyunya suke cin zarafin palastinawa tare da keta alfarmar qods.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Tashrin ta kasar Syria cewa, babban malami mai bayar da fatawar addinin muslunci a kasar Syria ya soki kasashen larabawa kan yadda suka nuna halin ko in kula kan dangane da yadda yahudawan sahyunya suke cin zarafin palastinawa tare da keta alfarmar qods mai alfarma.

A wani rahoton kuma shugaban kasar Siriya Bashar al-Asad ya yi kakkausar suka ga manyan kasashen duniya a kokarin da suke yi na haifar da zaman dar-dar a kasar, kamar yadda kuma ya soki lamirin matsayar kungiyar kasashen larabawa a kan kasar tasa yana mai cewa kungiyar ta zamanto wani kayan aiki a hannun 'yan wasu kasashen larabawa da suke son cimma manufarsu.
Shugaban na Siriya ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya yi wa al'ummar kasar a yau din nan a jami'ar Damaskus inda ya ce makircin da kungiyar larabawar take kulla wa kasarsa ya fi na sauran kasashen yammaci muni, yana mai cewa kasar tasa za ta ci gaba da zama 'yantacciya duk kuwa da makircin da ake kulla mata.
Har ila yau kuma shugaban na Siriya ya yi karin haske dangane da kokarin da wasu kasashen larabawan suke yi na murguda hakikanin abin da ke faruwa a kasar tasa ta hanyar kafafen watsa labaran da suka mallaka wanda ake ganin yana ishara ne da kasar Qatar da tashar talabijin din Al-Jazeera ta kasar Qatar din wacce ta yi kaurin suna wajen bayyana labaran da wasu suke ganin babu gaskiya cikinsu dangane da kasar Siriyan lamarin da ya sanya wasu ma'aikatan tashar barin aiki da tashar don nuna rashin amincewarsu da abin da tashar take yi.
Shugaban Siriya dai ya yi watsi da kiran da ya sauka da mulkin kasar yana mai sake kiran 'yan adawar kasar da su zo a zauna da su don tattauna hanyoyin da za a kawo sauyi cikin yadda ake gudanar da kasar.
932598
captcha