Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanr gizo na kamfanin dilalncin labaran kasar Kuwait KUNA cewa, kungiyar hadin kan kasashen larabawa ta yi kakakusar suka kan matakan da haramtacciyar kasar Isra'ila take dauka na cire muhimman abubuwan tarihin mulunci a cikin msallacin Qods ami alfarma.
A wani labarin an habarta cewa kotun kasa da kasa mai hukumta manyan laiffuka da ke helkawata a birnin Hague na kasar Holland ta ce mahukuntar kasar Libya sun gaza wajen amsa bukatar da ta gabatar musu na neman karin haske dangane da halin da dan tsohon shugaban kasar Libiyan Kanar Gaddafi wato Saiful Islam ya ke ciki.
Tun dai bayan kama Saiful Islam din ne kotun ta duniya ta bukaci gwamnatin Libya da ta bata damar ganawa da shi don sanin halin da ya ke ciki da kuma sanin ko gwamnatin Libya za ta mika mata shi domin yi masa shari'a bisa zargin da take masa na take hakkokin bil'adama da aikata laifuffukan yaki, sai dai kuma ta ce har ya zuwa yanzu dai kotun bata samu amsa a hukumance daga gwamnatin Libyan ba.
A yau ne dai wa'adin da kotun ta ba wa mahukuntan Libyan zai kare, to sai dai kuma sabbin mahukutan sun ce za su gurfanar da shi ne a kasar don hukumta shi lamarin da da dama suke sanya shakkun yiyuwar yi masa adalci a kasar musamman idan aka yi la'akari da yadda makomar mahaifinsa ta kasance.
A watan Nuwamban da ya gabata ne dai aka kama Saiful Islam din a kudancin Libyan sannan kuma ana ci gaba da tsare shi a garin Zintan. Ana ganin dai akwai yiyuwar kotun ta kai karar kasar Libyan kwamitin tsaron matukar dai ta ki amincewa da bukatar da ta gabatar mata.
932484