IQNA

Sayyid Nasrullah Ya Jadda Cewa Taron Arba'in Na Ashura A Ba'alabak Ya Dace Da Lokacin

12:46 - January 15, 2012
Lambar Labari: 2257031
Bangaren kasa da kasa, babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta hizbullag Sayyid Hassan Nasrullan ya jadda cewa gudanar da tarukan Ashura da aka yi garin Ba'alabak ya daidai da wannan lokaci na Arba'in saboda tarihin da wurin yake da shi.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Almanar cewa, babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta hizbullag Sayyid Hassan Nasrullan ya jadda cewa gudanar da tarukan Ashura da aka yi garin Ba'alabak ya daidai da wannan lokaci na Arba'in saboda tarihin da wurin yake da shi ta fuskacin Ashura.

Miliyoyin mutane ne su ke ci gaba da juyayin zagayowar kwanaki 40 na ashura a birnin Karbala na kasar Iraki, rahotannin da su ke fitowa daga Karbala sun ce ana hasashen cewa mutanen da su ka cika birnin sun haura miliyan 10, da su ka hada mutanen kasar da kuma bakin da su ka zo daga kasashen makwabta.

Miliyoyin Irakawa ne dai su ka ti tattaki da kafafunsu daga garuruwa masu nisa domin zuwa karbala., a gefe daya 'yan ta'adda sun rika kai hare-gare ga masu tafiyar zuwa karbala sai dai hakan bai hana mutane ci gaba da azamar isa hurumin imam Hussain (a.s.) ba.

A yau ma mutane 20 ne su ka yi shahada saboda harin da wani dan kunar bakin wake ya kai musu a garin Basra, wani jami'in yan sanda ya ce mutanen da aka kashe sun kai 20 yayin da wasu 15 su ka jikkata.

934638







captcha