Bangaren kasa da kasa, malaman addinin muslunci a kasar Iraki sun yi Allawadai da harin ta’addancin da aka kai kan miliyoyin mutanen da suka gudanar da tarukan cika kwanaki arba’in da shahadar Imam Hussain (AS) a yankunan kasar Iraki.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na ipairaq cewa, malaman addinin muslunci a kasar Iraki sun yi Allawadai da harin ta’addancin da aka kai kan miliyoyin mutanen da suka gudanar da tarukan cika kwanaki arba’in da shahadar Imam Hussain (AS) a yankunan kasar Iraki domin kawo cikas ga wadannan taruka.
Miliyoyin mutane ne su ke ci gaba da juyayin zagayowar kwanaki 40 na ashura a birnin Karbala na kasar Iraki, rahotannin da su ke fitowa daga Karbala sun ce ana hasashen cewa mutanen da su ka cika birnin sun haura miliyan 10, da su ka hada mutanen kasar da kuma bakin da su ka zo daga kasashen makwabta.
Miliyoyin Irakawa ne dai su ka ti tattaki da kafafunsu daga garuruwa masu nisa domin zuwa karbala.
A gefe daya 'yan ta'adda sun rika kai hare-gare ga masu tafiyar zuwa karbala sai dai hakan bai hana mutane ci gaba da azamar isa hurumin imam Hussain (a.s.) ba, a yau ma mutane 20 ne su ka yi shahada saboda harin da wani dan kunar bakin wake ya kai musu a garin Basra.
934981