IQNA

Kungiyar OIC Ta Yi Allawadai Da Harin Ta’addanci Kan Masallatan Palastinu

15:33 - January 16, 2012
Lambar Labari: 2257954
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kasashen musulmi ta yi kakkausar suka da yin Allawadai da haramtacciyar kasar Isra’ila kan harin ta’addancin da ta kai masallatan musulmi palastina a cikin yankunan gabar yamma da kogin Jordan.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadrawa na yanar gizo na CPI cewa, kungiyar kasashen musulmi ta yi kakkausar suka da yin Allawadai da haramtacciyar kasar Isra’ila kan harin ta’addancin da ta kai masallatan musulmi palastina a cikin yankunan gabar yamma da kogin Jordan a cikin wannan mako.
Kungiyar kare hakkin bil'adama ta kasa da kasa "Amnesty International "ta bukaci a gudanar da bincike akan kisan da jami'an tsaro su ka yi wa wani mai zanga-zanga a gabacin saudiyya, a wani bayani da kungiyar ta kare hakkin bil'adama ta fitar ta bukaci a yi bincike mai zaman kanshi akan kisan da aka yi wa Isam Muhammad Abu Abdullah a lokacin da ya ke cikin zanga-zanga a garin Awamiyyah da ke gabacin Saudiyya.
Bayanin kungiyar ya ci gaba da cewa: "Zanga-zangar ranar alhamis din da ta gabata an yi ta ne domin kira da a saki fursunonin siyasa da ake tsare da su da kuma kawo karshen wariyar da ake yi wa 'yan shi'a a yankin, a cikin watannin bayan nan dai jami'an tsaron Saudiyya sun rika bude wuta akan masu zanga-zangar lumana da su ke son a samar sa sauye-sauye na siyasa a cikin kasar.
934831

captcha