Bangaren kasa da kasa, an kawo karshen bababn taron mabiya addinin muslunci na kasar Bangaladash a kusa da birnin Dakar, wanda ya samu halartar miliyoyin musulmi inda aka yi kira zuwa ga hadin kai tsakanin dukaknin al'ummar musulmi baki daya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na news 3 cewa, an kawo karshen bababn taron mabiya addinin muslunci na kasar Bangaladash a kusa da birnin Dakar, wanda ya samu halartar miliyoyin musulmi inda aka yi kira zuwa ga hadin kai tsakanin dukaknin al'ummar musulmi baki daya da suke yankin.
A wani labarin kuma hukumomi a kasar India sun bada sanarwan cewa dukkan ma'aikatan jirgin ruwan kasar Mai suna MT Fairchem guda 21 wadanda yan fashi daga kasar Somalia suka sashe su a cikin watan Augustan bara sun kubuta daga hannun yan fashin ba tare da ko kwarzane ba.
Directa mai kula da harkokin zirga zirgan jiragen ruwa na kasar India a birnin Mumbai ne ya bayyana haka a ranar Asabar da yamma, kuma ya kara da cewa dukkan ma'aikatan 21 tare da jirgin nasu duk sun kubuta daga hannun yan fashin.
A ranar 20-Augustan shekarar bara ne dai yan fashi daga kasar Somalia suka yi garkuwa da jirgin a lokacinda yake kokarin isar tashir jiragen ruwa na salalah dake kasar Qatar.
Majiyar ma'aikatar bai bayyana ko ta bada kudin fansa ga yan fashin kafin su salami mutanen ba. Yan fashin dai suna samun miliyoyin dalar Amurka kudin fansa a mafi yawan fashin da suke yi a cikin teku kafin su sake wadanda suke garkuwa da su.
936047