Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-manar cewa, shugaban tawagar kungiyar gwagwarmayar hizbullah a majalisar dokokin kasar Lebanon ya bayyan amatakin sakataren majalisar dinkin duniya ya dauka aziyararsa a kasar Lebanon da cewa abin ban takaici ne domin kuwa ya tabbatar da cewa babu wani da ke hannunsa a cikin abubuwan da yake fada, shi sdan sakon Amurka da yahudawa ne.
Babban Magatarda na Majalisar Doinkin Duniya Ban Ki-moon ya soma wata ziyarar aiki ta tsawon kwanaki uku a kasar Labanan daga yau juma'a, domin tattauna batutuwan da suka shafi rikicin siyasar kasar Syria, da matsayin kotun da kasashen duniya suka kafa domin binciken kisan da aka yi tsohon Firayi ministan kasar ta Labanan Rafikul Hariri da kuma neman gwamnatin Labanan ta karbe illahirin makamai da kungiyar Hizbullah ta mallaka a cikin kasar.
Ban Ki-Moon zai gana da shugaban kasar ta Labanan Mishel Suleman, da Firaministan kasar Najib Mikati, da kuma shugaban Majalisar dokokin kasar Nahbih Beri wanda babban abokin kawance ne ga kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hizbullah, yayin da a gobe asabar zai gana da manyan kwadojin rundunar wanzar da tsaro.
936682