IQNA

18:18 - January 28, 2012
Lambar Labari: 2263540
Bangaren kasa da kasa, bayan watsa wani labari da ke cewa masarautar kasar Bahrain na shirin kama shugaban majalisar malaman addinin muslunci ta kasar Ayatollah Sheikh Isa Kasim majalisar ta ja kunnen masarautar da ta shiga taitayinta.
Kamfanin dilalncin labaran oiqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-manar cewa, bayan watsa wani labari da ke cewa masarautar kasar Bahrain na shirin kama shugaban majalisar malaman addinin muslunci ta kasar Ayatollah Sheikh Isa Kasim majalisar ta ja kunnen masarautar da ta shiga taitayinta dangane da duk wani mataki da za ta dauka kan wannan bakar aniya.
Wanann mataki da masarautar kasar Bahrain ke neman dauka kan shehin malami baya rasa nasaba da irin kiran da yake yi ne ga mahukuntan da su saurari bukatun mutane domin warware takaddamar da ake fama da ita, maimakon yin amfani da karfin tuwo wajen murkushe fararen hula masu neman ahkkokinsu da aka haramta musu.
Bayan watsa wani labari da ke cewa masarautar kasar Bahrain na shirin kama shugaban majalisar malaman addinin muslunci ta kasar Ayatollah Sheikh Isa Kasim majalisar ta ja kunnen masarautar da ta kwana da sanin cewa, duk abin da ya samu malamin to zai kare a kanta ne.
Al’ummar Bahrain dai kamar sauran al’ummomin larabawa suna neman hakkokinsu ne da aka haramta musu ta hanyar lumana, amma mahukuntan kasar tare da na kasar Saudiyya da kuma taimakon Amurka da Birtaniya, suna ci gaba da murkushe masu zanga-zangar. 941388
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: