IQNA

18:19 - January 28, 2012
Lambar Labari: 2263547
Bangaren kasa da kasa, wani shaharraren dan wasan fina-finai a kamfanin hollywood na kasar Amurka ya sanar cewa yana shirin karbar addinin muslunci nan ba da jimawa ba bayan da ya gudanar da bincike kan wannan addini kuma ya gamsu da shi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na emarrakech cewa, Liam Nison wani shaharraren dan wasan fina-finai a kamfanin hollywood na kasar Amurka ya sanar cewa yana shirin karbar addinin muslunci nan ba da jimawa ba bayan da ya gudanar da bincike kan wannan addini kuma ya gamsu da shi, kamar dai yadda ya bayyana a zantawarsa da mujallar the sun.
Liam son ya ce ya shiga cikin wani finm da aka yi a kasar Turkiya, kuma dukaknin wadanda ya yi wasa tare da su mabiya addinin muslunci ne, kuma yadda ya ga suna kiyaye abubuwa na addininsu ya burge shi, wannan ne ya sanya shi yin bincike kan addinin muslunci da kuma abubuwan da yake koyarwa a cikin akidunsa, kuma ya gamsu da akidar muslunci.
Ya jadda cewa nan ba da jimawa ba zai sanar da musluncinsa a fili domin kowa ya san y matsayinsa, ya ce daga cikin abubuwan da suka burge shi har da yadda ya ga musulmi suna yn sallah, wanda hakan ya yi tasirin cikin zuciyarsa, bayan nan kuma ya ziyarci wyrare na tarihi a cikin kasar ta Turkiya, da ke tabbatar da cewa addinin muslunci ya taka gaggarumar rawa wajen shiryar da dan adam zuwa sahihin tafarki na rayuwa. 941298
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: