Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya habarta cewa, a wata zantawa day a yi da wani masani Faiz Bu shamala ya bayyana cewa, a daidai lokacin da kasashen larabawa da na musulmi suka shagaltu da hidimominsu an cikin gida musamman ma rikicn siyasa da murkushe masu neman sauyi yahudawan sahyuniya suna hankoron ganin sun mamaye yankunan musulmi da na arabawa da ke birnin Qods da sauran wurare masu tsari da suke cikin yankin Palastinu.
A wani labarin kuma Sakataren kungiyar hadin kan kasashen larabawa tare da pira ministan kasar sun nufi kasar Amurka domin neman goyon kwamitin tsaron majalisar dinkn duniya a hankoron da suke yin a neman ganin bayan shugaba Bashar Asad na kasar Syria.
A lokacin da yake barin birnin Alkahira a yau, sakaren kungiyar hadin kan kasashen larabawa Nabil Al-arabi ya sheda ma manema labarai cewa za su halarci zaman kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya a ranar Talata mai zuwa, domin neman mambobin kwamitin su amince da wannan aniya ta kasashen larabawa, da ke neman shugaba Asad ya safka daga kan karagar mulki.
Tuni kasashen Amurka da Birtaniya da Faransa gami da Jamus suka nuna matukar farin cikinsu da wannan bukata ta kasashen larabawa, kuma suna shirin amincewa da hakan a gaban kwamitin tsaron, amma kasashen Rasha da China sun ce wannan daftarin kudiri na kasashen larabawa babu adalci a cikinsa, domin kuwa ya dora alhakin abin da ke faruwa kan Bashar Asad ne kawai, ba tare da ambaton 'yan bindiga da suke kai hare-hare kan jami'an tsaro da fararen hular kasar Syria ba.
937697