Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin yanar gizo na kamfanin dilalncin labaran Trend cewa an yi wa wasu daga cikin kungiyoyi da cibiyoyi na addini da ma wasu kadan da ba na addini ba rijista a kasar Azarbaijan a hankoron da gwamnatin kasar take yi na ganin cewa ta takaita da dama daga cikin ayyukan addinin muslunci a kasar wadda ta kwashe tsawon shekaru tana bin salon mulki da babu ruwansa da addini.
Shugaban ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar palastinu Khalid Mus’al ya gana da babban malamin jami’ar Azahar da ke birnin Alkahira na kasar Masar dangane da abubuwan da suke faruwa a yankin baki daya musamman ma a yankin gabas ta tsakiya.
An gudanar da tarukan cika shekara guda da samun nasarar juyin juya hali a kasar Tunisia tare da halartar dubban daruruwan mutane da suka gudanar da zanga-zangar goyion baya ga juyi da kuma yin Allawadai da halaratr sarkin Qatar a wurin wadannan taruka.
A jiya ne aka gudanar da tarukan cika shekara guda da samun nasarar juyin juya hali a kasar Tunisia, wanda ya kawo karshen mulkin kama karya na tsohon shugaban kasar Zainul Abidin Bin Ali.
Mai aiko ma gidan talabijin Al-alam rahotanni daga kasar Tunisia ya habarta cewa, a daidai lokacin da ake gudanar da tarukan a hukumance a birnin Tunis, dubban mutane sun gudanar da zanga-zanga a wasu biranan kasar, inda suka yi Allawadai da ziyarar sarki Qatar a kasarsu, wanda yake halartar bukukuwan cika shekara guda da samun juyi a kasar. 945227