Bangaren kasa da kasa; komitin kasa mai sa ido kan musulunci da yadda ake takurawa musulmi da kuma masu tsananin adawa da musulunci a Faransa ya bayyana cewa: an samu karuwar masu daukan matakan adawa da musulunci a kasar Faransa a shekara ta dubu biyu da goma sha daya da kasha talatin da hudu bias dari idan aka kwatamta da shekara ta dubu biyu da goma.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: komitin kasa mai sa ido kan musulunci da yadda ake takurawa musulmi da kuma masu tsananin adawa da musulunci a Faransa ya bayyana cewa: an samu karuwar masu daukan matakan adawa da musulunci a kasar Faransa a shekara ta dubu biyu da goma sha daya da kasha talatin da hudu bias dari idan aka kwatamta da shekara ta dubu biyu da goma.Abdallah Zikri shugaban komitin sa ido kan wannan matsala ya yi Karin bayani da cewa ya kamata mahukumta a kasar faransa su tashi haikan domin kawo karshen wannan lamari musamman idan aka yi la'akari da yadda wannan matsala ke kara kamari a wannan kasa da kuma yadda musulmi ke fuskantar nuna karan tsana da takurawa daga tsurarun yan faransa masu adawa da addinin musulunci.
946117