Bangaren kasa da kasa, majalisar malaman addinin muslunci a kasar Sudan ta fitar da wani bayani da a cikinsa take cewa al’ummar kasar ba su bukatar wani abu ya zama tsarinsu na rayuwa tare da yin kira da a kara baiwa wannan bangare muhimmanci a matukar a cikin dukaknin harkokin mulki da siyasa.
Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na sudaneseonline ccewa, majalisar malaman addinin muslunci a kasar Sudan ta fitar da wani bayani da a cikinsa take cewa al’ummar kasar ba su bukatar wani abu ya zama tsarinsu na rayuwa tare da yin kira da a kara baiwa wannan bangare muhimmanci a matukar a cikin dukaknin harkokin mulki da siyasa a fadin kasar.
A bangare guda kuma gwamnatin Sudan ta musanta cewa; jiragen saman yakinta sun kai hare-hare kan 'yan tawaye a yankunan jihohin kudancin Kordofan da Blue Nile.
Kakakin rundunar sojin kasar Sudan ya bayyana cewar sojojin gwamnatin Sudan ba su kaddamar da wani hari kan 'yan tawayen kasar ba a cikin 'yan kwanakin nan, ballantana kai hare-hare kan yankunan jihohin kudancin Kordofan da Blue Nile, don haka da'awar kasar Amurka na cewa sojojin gwamnatin Sudan sun kai hare-hare kan yankunan jihohin biyu karya ce tsagwaronta.
A ranar juma'ar da ta gabata ce dai jakadiyar kasar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Suzan Rice ta yi da'awar cewa; sojojin gwamnatin Sudan sun kai hare-hare kan yankunan jihohin kudancin Kordofan da Blue Nile, tare da yin Allah wadai da hare-haren.
946726