IQNA

An Bude Makabarta Ta Farko Mallakin Mabiya Addinin Muslunci A Kasar Faransa

18:07 - February 07, 2012
Lambar Labari: 2270660
Bangaren kasa da kasa, an bude wata makabarta wadda ita ce irin ta ta farko da aka bude a kasar Faransa domin buzne mabiya addinin muslunci da suka rasa rayukansu a kasar, kuma an bude wannan makabarta ne a birnin Strasburg da ke kasar.
Kamfanin diallncin labaran iqna ya habarta cewa ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizoa na kamfanin dilalncin labaran safir News cewa, an bude wata makabarta wadda ita ce irin ta ta farko da aka bude a kasar Faransa domin buzne mabiya addinin muslunci da suka rasa rayukansu a kasar, kuma an bude wannan makabarta ne a birnin Strasburg da ke kasar ta Faransa.
A wani labarin kuma na daban kungiyar kare hakkin bil'adama ta kasa da kasa "Amnesty International "ta bukaci a gudanar da bincike akan kisan da jami'an tsaro su ka yi wa wani mai zanga-zanga a gabacin saudiyya, a wani bayani da kungiyar ta kare hakkin bil'adama ta fitar ta bukaci a yi bincike mai zaman kanshi akan kisan da aka yi wa Isam Muhammad Abu Abdullah a lokacin da ya ke cikin zanga-zanga a garin Awamiyyah da ke gabacin Saudiyya.
Bayanin kungiyar ya ci gaba da cewa: "Zanga-zangar ranar alhamis din da ta gabata an yi ta ne domin kira da a saki fursunonin siyasa da ake tsare da su da kuma kawo karshen wariyar da ake yi wa 'yan shi'a a yankin, a cikin watannin bayan nan dai jami'an tsaron Saudiyya sun rika bude wuta akan masu zanga-zangar lumana da su ke son a samar sa sauye-sauye na siyasa a cikin kasar.
948253

captcha