IQNA

Kwamitin mabiya addinan kiristanci da Muslunci Sun Yi Allawadai Da Isra'ila

14:31 - February 08, 2012
Lambar Labari: 2271212
Bangaren kasa da kasa, babban kwamitin kula da harkokin musulmi da kuma mabiya addinin kirista a birnin Qods mai alfarma ya yi kakakusar suka da yin Allawadai da haramtacciyar kasar Isra'ila dangane da matakan da take dauka na yahudantar da birnin mai alfarma.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, babban kwamitin kula da harkokin musulmi da kuma mabiya addinin kirista a birnin Qods mai alfarma ya yi kakakusar suka da yin Allawadai da haramtacciyar kasar Isra'ila dangane da matakan da take dauka na yahudantar da birnin mai alfarma wanda yake da wurare na tarihi ga dukkanin addinan biyu.
A bangare guda kuma dangane da zaman tattaunawar sulhu da ta gudana tsakanin Hamas ta Fatah a birnin Doha na kasar Qatar, inda wasu daga cikin palastinawa musamman 'yan gwagwarmaya daga cikinsu, suke kallon haka a matsayi wani mataki na mika kai ga manufar HKI.
Fitattacen marubucin nan na palastinu kuma mai goyon bayan gwagwarmaya Mu'in Al-manna, ya bayyana cewa yadda aka gudanar da wannan tattaunawa da kuma yarjejeniyar da aka cimmawa ta kafa gwamnatin rikon kwarya a karkashin Mahmud Abbas, na tattare da alamar tambaya, domin kuwa suna kallon Mahmud Abbas a matsayin wanda ya rusa dukkanin yarjeniyoyin da aka cimmawa a lokutan baya, kuma yanzu an mika masa wuka da nama.
A bangare guda kuma wasu bayann na nuni da cewa wasu daga mambobin kungiyar Hamas ba su amince da yarjejeniyar Doha ba, domin kuwa sun yi imanin cewa gwamnatin Qatar tana kare manufofin HKI ne a yankin, kuma ba ta taba yin wani abu domin amfanin palastinawa ko maslaharsu ba, saboda haka suna ganin akwai wata makarkashiya da aka shirya domin jefa Hamas cikin tarko.
949090

captcha