IQNA

Musulmin Gabacin Afirka Sun Gudanar da Zanga-Zangar Yin Allawadai da Takunkumi Kan Iran

14:30 - February 08, 2012
Lambar Labari: 2271214
Bangaren kasa da kasa, Musulmi a wasu kasashen gabacin nahiyar Afirka sun gudanar da zanga-zanga yin Allawadai da la'antar kasashen turai dangane das aka takunkumin karya tattalin arziki a kan jamhuriyar muslunci ta Iran.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cewa, Musulmi a wasu kasashen gabacin nahiyar Afirka sun gudanar da zanga-zanga yin Allawadai da la'antar kasashen turai dangane das aka takunkumin karya tattalin arziki a kan jamhuriyar muslunci ta Iran wanda aka yi a cikin kwanakin.
Rasha ta ja kunnen gwamnatin Amurka dangane da matsin lambar take yi kan kasashn Iran da Syria saboda wasu dalilai kawai na siyasa, a cikin wani bayani da ta fitar, ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta yi kakakusar suka kan yadda gwamnatin Amurka take matsa lamba kan kasashen Syria da Iran, tare da yada karairayi a kafofin yada labarai na Amurka da kasashen yammacin turai dangane da wadannan kasashe, da kuma yadda ake danganta shirin Iran na makamashin nukiliya da kasar Rasha.
Bayanin ya ce dukaknin matsin lambar da take yi wa Iran ba ya da wata dangataka shirinta na makamshin nukiliya, dalilin hakan shi ne Iran taki mika kai ga manufofin siyasar kasar Amurka da sauran kasashen turai, kamar yadda wasu daga cikin manyan kasashen musulmi suke yi, inda bayanin ya buga misali da Saudiyya da Qatar, wadanda su ne manyan aminan Amurka a yankin gabas ta tsakiya baki daya.
949047
captcha