Bangaren kasa da kasa, jam’iyyar Likud mai tsananin tsatsauran ra’yi kan akidar sahyuniyanci ta kudiri aniyar kaddamar da wani farmaki kan masallacin Qods mai alfarma da nufin rushe wurare masu tsarki a wurin muslumi da kuma mabiya addinin kirista.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin saddarwa na yanar gizo na CPI cewa, jam’iyyar Likud mai tsananin tsatsauran ra’yi kan akidar sahyuniyanci ta kudiri aniyar kaddamar da wani farmaki kan masallacin Qods mai alfarma da nufin rushe wurare masu tsarki a wurin muslumi da kuma mabiya addinin kirista ta hanyar yin amfani da ‘yan bangar wannan jamiyya.
Bangare guda kuma shugaban majalisar muslunci mai kula da ayyukan da suka danganci batun ‘yantar da palastinu daga mamayar yahudawa Muhammad Namir ya sheda cewa, gwagwarmayar muslunci ce ta hana mayar da birinin Qods mai alfarma babban birnin yahudawa.
A wata zantawa da ta hada shi da kamfanin dilalncin labaran iqna, shugaban majalisar muslunci mai kula da ayyukan da suka danganci batun ‘yantar da palastinu daga mamayar yahudawa Muhammad Namir ya sheda cewa, gwagwarmayar muslunci ce ta hana mayar da birinin Qods mai alfarma babban birnin yahudawa kamar yadda suka shirya.
951092