IQNA

19:57 - February 13, 2012
Lambar Labari: 2273580
Bangaren kas ada kasa, malaman mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka akasar Saudiyya sun kakkausar suka kan mahukuntan kasar dangane da kisan kiyashin da suke yi wa masu zanga-zangar neman hakkokinsu da aka haramta musu a kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na rasid cewa, da dama daga cikin malaman mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka akasar Saudiyya sun kakkausar suka kan mahukuntan kasar dangane da kisan kiyashin da suke yi wa masu zanga-zangar neman hakkokinsu da aka haramta musu a kasar ta Saudiyya.
Haka nan kuma an ya nakalto daga shafin sadrawa an yanar gizo na Nun cewa, Fathi shazili tsohon jakadan kasar Masar a Saudiyya ya bayyana cewa cin zarafin mabiya tafarkin mazhabar shi’a da ake yi a kasar Saudiyya ya wuce haddi, kuma kasashen duniya suna kallo sun yi gum da bakunansu, domin kuwa gwamnatin Amurka tana goyon bayan Saudiyya kan ta’asar da take tafkawa.
Mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka akasar Saudiyya sun kakkausar suka kan mahukuntan kasar dangane da kisan kiyashin da suke yi wa masu zanga-zangar neman hakkokinsu da aka haramta musu, sakamakon danne su da wahabiyan kasar ke yi.
951843
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: