IQNA

Kungiyar Hizbullah Ta Yi Allawadai Da Harin Jami’an Tsaro Kan Gidan Sheikh Salman

19:55 - February 13, 2012
Lambar Labari: 2273583
Bangaren kasa da kasa, kungiyar gwagwarmayar kasar Lebanon ta hzib ullah ta yi kakakusar suka da yin Allawadai da kai harin da jami’an tsaro gami da ‘yan bangar masarautar Baharain suka yi kan gidan sakataren jamiyar wifaq ta kasar Bahrain a jiya.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Almanar cewa, kungiyar gwagwarmayar kasar Lebanon ta hzib ullah ta yi kakakusar suka da yin Allawadai da kai harin da jami’an tsaro gami da ‘yan bangar masarautar Baharain suka yi kan gidan sakataren jamiyar wifaq ta kasar Bahrain, a yankurin mahukuntar tare da taimakon AMURKA DA Saudiyya suke yi na ganin sun murkushe masu neman sauyi.
B bayan watsa wani labari da ke cewa masarautar kasar Bahrain na shirin kama shugaban majalisar malaman addinin muslunci ta kasar Ayatollah Sheikh Isa Kasim majalisar ta ja kunnen masarautar da ta shiga taitayinta dangane da duk wani mataki da za ta dauka kan wannan bakar aniya.
Wanann mataki da masarautar kasar Bahrain ke neman dauka kan shehin malami baya rasa nasaba da irin kiran da yake yi ne ga mahukuntan da su saurari bukatun mutane domin warware takaddamar da ake fama da ita, maimakon yin amfani da karfin tuwo wajen murkushe fararen hula masu neman ahkkokinsu da aka haramta musu.
Bayan watsa wani labari da ke cewa masarautar kasar Bahrain na shirin kama shugaban majalisar malaman addinin muslunci ta kasar Ayatollah Sheikh Isa Kasim majalisar ta ja kunnen masarautar da ta kwana da sanin cewa, duk abin da ya samu malamin to zai kare a kanta ne.
Al’ummar Bahrain dai kamar sauran al’ummomin larabawa suna neman hakkokinsu ne da aka haramta musu ta hanyar lumana, amma mahukuntan kasar tare da na kasar Saudiyya da kuma taimakon Amurka da Birtaniya, suna ci gaba da murkushe masu zanga-zangar.
951604


captcha