Bangaren kasa da kasa, Malazia za ta dauki nauyin shirya gudanar da zaman taro na kasashen duniya kan kayan halal wanda shi ne karo na bakwai da za agudanar da wannan taro tare da halartar wakilai daga kasashen duniya, da suka hada da na musulmi da ma wadamnda ba na musulmi ba.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na asidcom cewa, Malazia za ta dauki nauyin shirya gudanar da zaman taro na kasashen duniya kan kayan halal wanda shi ne karo na bakwai da za agudanar da wannan taro tare da halartar wakilai daga kasashen duniya, da suka hada da na musulmi da ma wadanda ba na musulmi ba, gami da wakilan kamfanoni na kasashen malamzia China da sauransu.
A wani labarin kuma pira ministan yankin gaza a Palastinu Isma’il Haniyya ya bayyana cewa, yankin gabas ta tsakiya ya zama wani wurin buga misali da gwagwarmayar neman ‘yanci da fita daga karshin mulkin zalunci da kama karyana azzaluman shugabanni da sarakuna.
Haniyya ya byayana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi ga al’ummar kasar Tunisia a ziyarar da yake gudanarwa a wasui daga cikin kasashen yankin da suka hada Masar da kuma Suda gami da Turkiya, inda yake jadda matsayin kungiyar gwagwarmaya ta Hamas wajen ci gaba da yin gwagwarmaya domin samun ‘yancin al’ummar yankin.
Pira ministan yankin gaza a Palastinu Isma’il Haniyya ya bayyana cewa, yankin gabas ta tsakiya ya zama wani wurin buga misali da gwagwarmayar neman ‘yanci da fita daga karshin mulkin zalunci da kama karya azzaluman shugabanninsu da suke azurta kansu da dukiyoyin da al’ummar kasar suke da su.
953320