IQNA

18:07 - February 16, 2012
Lambar Labari: 2275347
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani taro na hadin gwiwa tsakanin malaman mabiya addinan kiristanci da muslunci domin kare masallacin Qods mai alfarma daga barazanar yahudawan sahyuniya da suke yi a cikin 'yan lokutanan a kan wannan wuri mai albarka.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Alyaum sabi cewa, za a gudanar da wani taro na hadin gwiwa tsakanin malaman mabiya addinan kiristanci da muslunci domin kare masallacin Qods mai alfarma daga barazanar yahudawan sahyuniya da suke yi a cikin 'yan lokutanan a kan wannan wuri mai albarka inda suka fara rusa wani bangare na masallaci.
A cikin wannan makon ne kwamitin tsara sabon kundin tsarin mulkin ya kammala aikinsa, kuma ya mika shi ga shugaba Bashar Asad domin yin dubi a cikinsa, daga nan kuma za a mika shi ga majalisar dokokin kasar, bayan nan za a ji ra'ayin jamar kasar a kansa.

Sabon kundin tsarin mulkin kasar ta Syria dai yana dauke ne da canje-canje da dama ta fuskacin harkokin siyasa da mulki a kasar, wanda ake ganin cewa idan har aka amince da shi a matsayin kundin tsarin mulki a kasar, to zai zama abin buga misali da shi ta fuskar demokradiyya a cikin kasashen kasashen larabawa.

Daga cikin muhimman abubuwan da sabon kundin tsarin mulkin na kasar Syria ya kunsa, har da dokar kayyade wa'adin shugabancin kasar a cikin shekaru bakwai, kuma za a iya zabar shugaba a wa'ai na biyu, amma daga nan ba zai sake yin shugabanci a kasar ba.

Sa'anan kuma al'umma ne za su zabi shugaban kasa da kansu, maimakon zaben shi a majlaisar dokoki, kamar yadda sabon kundin tsarin mulkin ya bayar da damar kafa jam'iyun siyasa ba tare da wani haddi ba, kuma babu wani fifiko ga wata jam'iyya a kan wata. Haka nan kuma shugaban kasa dole addininsa ya zama muslunci, amma bisa sharadin zai girmama sauran addinai da ke kasar naki daya ba tare da nuna banbanci a tsakanin mabiyansu ba.
953855
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: