IQNA

Mabiya Tafarkin Mazhabar Shi'a A Bahrain Sun Shiga Wani Sabon Babi Na Siyasa

18:07 - February 16, 2012
Lambar Labari: 2275352
Bangaren kasa da kasa, mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah da suke a kasar Bahrain sun shiga wani sabon babi na siyasa a kasar bayan share kimanin shekara guda suna gudanar da bore na neman 'yanci da kuma hakkokinsu da aka haramta musu na 'yan kasa.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah da suke a kasar Bahrain sun shiga wani sabon babi na siyasa a kasar bayan share kimanin shekara guda suna gudanar da bore na neman 'yanci da kuma hakkokinsu da aka haramta musu na 'yan kasa a hannun sarkin kasar da ya shahara da kama karya.
Makiyan al'umma da su ka nutse cikin son abin duniya suna kallo al'uma a matsayin bayinsu saboda haka su ke kokarin bautar da su domin cimma manufofinsu.Amerika da ‘yan hasayoniya sannan kuma da taimakon ‘yan kanzaginsu a cikin wannan yankin sun zage damtse domin su karkatar da manufofin yunkurin al'umma na hakika acikin wannan yankin. Babban fatarsu kuwa shi ne su ci gaba da shimfida ikonsa akan kasar Masar. Sai dai a lokaci guda muna ganin yadda al'ummun Bahrain da YAmen da Libya su ke ci gaba da yin tsayin daka akan manufofinsu. Har yanzu al'ummu acikin wadannan kasashen ba su ja da baya ba, suna ci gaba da kalubalantar mulkin mallaka na cikin gida da kuma waje.
Sun gaskata alkawalin Ubangiji da ya zo acikin kur'ani akan musulmi akan cewa jurewa wahala sakamakonsa sauki da nasara. Ya zo acikin aya ta 186 a suratu Ali imrana cewa: "Idan ku yi tsayin daka kuma zama masu tsoron Allah to hakan yana daga cikin al'amurra masu karko da kuma samun nutsuwa.
Abin tambaya anan shi ne ko wadanne hanyoyi ne yammacin turai din ke amfani da su domin kashe kaifin yunkurin juyin da kuma karkatar da shi? Kuma menene mafita a gaban al'ummun da su ke yin wannan yunkurin.
953501



captcha