Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dilalncin labaran kasae Malazia cewa, an fara gudanar da wani zaman taro kan harkokin tattalin arziki a kasar Malazia tare da halartar wakilan kasashen musulmi da suke ammbobi a kungiyar bunkasa tatatlin arzikin musulmi a karkashin kungiyar hadin kan musulmi ta duniya.
A cikin wannan makon ne kwamitin tsara sabon kundin tsarin mulkin ya kammala aikinsa, kuma ya mika shi ga shugaba Bashar Asad domin yin dubi a cikinsa, daga nan kuma za a mika shi ga majalisar dokokin kasar, bayan nan za a ji ra'ayin jamar kasar a kansa.
Sabon kundin tsarin mulkin kasar ta Syria dai yana dauke ne da canje-canje da dama ta fuskacin harkokin siyasa da mulki a kasar, wanda ake ganin cewa idan har aka amince da shi a matsayin kundin tsarin mulki a kasar, to zai zama abin buga misali da shi ta fuskar demokradiyya a cikin kasashen kasashen larabawa.
Daga cikin muhimman abubuwan da sabon kundin tsarin mulkin na kasar Syria ya kunsa, har da dokar kayyade wa'adin shugabancin kasar a cikin shekaru bakwai, kuma za a iya zabar shugaba a wa'ai na biyu, amma daga nan ba zai sake yin shugabanci a kasar ba.
954837