Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labaransa a yankin Asia cewa, an bayar da lasisi ga kungiyoyin addinin muslunci kimanin arba’in da bakwai 47 domin gudanar da ayyuaknsu cikin izini a kasar Tajikistan kamar dai yadda ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar ta sanar a cikin wani bayani da ta fitar.
A karon farko ana shirin gudanar da wani shiri da aka kira da yunkurin nuna goyon baya ga masallacin Qods ta hanayar sadarwa wanda hakan shi ne karon farko da masana a wannan bangaren za su gudanar da irin wannan shiri a mataki na kasa da kasa.
Ita kuwa kungiyar kasashen musulmi ta yi kakkausar suka da yin Allawadai da haramtacciyar kasar Isra’ila kan harin ta’addancin da ta kai masallatan musulmi palastina a cikin yankunan gabar yamma da kogin Jordan a cikin wannan mako da muke ciki.
A nata bangare kungiyar kare hakkin bil'adama ta kasa da kasa "Amnesty International "ta bukaci a gudanar da bincike akan kisan da jami'an tsaro su ka yi wa wani mai zanga-zanga a gabacin saudiyya, a wani bayani da kungiyar ta kare hakkin bil'adama ta fitar ta bukaci a yi bincike mai zaman kanshi akan kisan da aka yi wa Isam Muhammad Abu Abdullah a lokacin da ya ke cikin zanga-zanga a garin Awamiyyah da ke gabacin kasar.
955273