IQNA

Za A Gyara Masallacin Farko A Musulunci Da Ke Yankin Quba A Kusa Da Madina

16:50 - February 22, 2012
Lambar Labari: 2279116
Bangaren kasa da kasa, ana shirin fara gyaran masallacin Quba wanda shi ne masallacin farko a cikin addinin muslunci da ke kan hanyar isa birnin madina daga Makka kamar dai yadda maa'ikatar kula da harkokin addini ta kasar Saudiyya ta sanar.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na IINA cewa, ana shirin fara gyaran masallacin Quba wanda shi ne masallacin farko a cikin addinin muslunci da ke kan hanyar isa birnin madina daga Makka kamar dai yadda maa'ikatar kula da harkokin addini ta kasar Saudiyya ta sanar a cikin wani bayani da ta fitar.
A wani labarin kuma babban kwamnadan sojojin Rasha a yankin San Betrasburg janar Arkady Bakhin ya sheda cewa, ma'aikatar tsaron kasar ta mika musu makaman kariya da za su fara aiki a cikin 'yan makonni masu zuwa.
A wani rahoto da kamfanin dillancin labaran Raya Nofosty na kasar Rahs aya bayar an bayyana cewa, babban hafsan hafsoshin sojin kasar Rasha Janar Alexender Zelin ya sanar cewa, za su kafa makaman kariya a cikin wannan shekara a kan iyakokin kasar Rasha, domin zama cikin shirin fuskantar duk wata barazana daga wajen kasar.
Wannan dai shi ne karon farko da kasar Rasha ta fitar da wadannan makamai na domin girka su, wadanda kuma ita kadai ce ta mallki irinsu a duniya. Ana ganin dai wannan mataki da Rasha ta dauka ba ya rasa nasaba da girka makaman da kasashen turai suka yi ne a wasu kasashen gabacin nahiyar, wanda rasha take kallon hakan a matsayin wata babbar barazana gare ta. 957629



captcha